Labarai
Majalisar Zamfara Ta Tsawaita Dakatarwar ‘Yan Majalisar Jihar 7
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta tsawaita dakatarwar wasu ‘yan majalisa bakwai daga ayyukan majalisa zuwa wani sabon zangon zaman majalisa.
An ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar da Kakakin majalisa, Bilyaminu Ismail Moriki, ya jagoranta a yau.
Wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Kakakin Majalisar, Bello Madaro Kurya, ta ce ‘yan majalisar da abin ya shafa na fuskantar bincike kan zargin rashin da’a da kuma saba ƙa’idojin majalisa.
An tsawaita dakatarwar ne bayan kudirin da Shugaban Masu Rinjaye, Bello Muhammad Mazawajje na Tsafe ta Gabas, ya gabatar, wanda Ibrahim Garba Liman na Gusau II ya mara wa baya.
Masu gabatar da kudirin sun bayyana cewa duk da cikar lokacin dakatarwar farko, akwai shari’a a gaban kotu da ke bukatar a ci gaba da matakin har sai an kammala shari’ar.
Majalisar ta amince da kudirin baki ɗaya, sannan Kakakin Majalisar ya sanar da sunayen ‘yan majalisar bakwai da abin ya shafa.
A wani cigaba kuma, majalisar ta karɓi ƙudirin dokoki uku daga bangaren zartarwa domin nazari da aiki a kai.
Daya daga cikin muhimman kudirorin na neman kafa tsarin biyan fansho, alawus-alawus da hakkokin tsofaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, kakakin majalisa da mataimakinsa, tare da wasu dokoki na gudanarwa.
Majalisar ta kuma amince da tsarin aikinta na shekarar 2026/2027, bisa bin sashe na 104 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Bayan haka, majalisar ta tafi hutun zaman majalisa.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
