Connect with us

Labarai

Rukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki

Published

on

Daga Sani Dutsinma 

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi bankwana da rukuni na farko na maniyyata 418 daga jihar da suka tashi  zuwa ƙasar Saudiyya domin fara aikin Hajjin shekarar 2026.

Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tashinsu a Filin Jirgin Sama na Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, Gwamna Idris ya nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba su damar halartar aikin Hajjin bana.

Gwamna Nasir Idris ya buƙaci su kasance jakadu nagari na jihar da ma Najeriya gaba ɗaya a duk tsawon zamansu a ƙasa mai tsarki, tare da yin kira a garesu da su yi addu’ar zaman lafiya a Jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya.

Jirgi na farko ya tashi ne da yammacin ranar Lahadi, ɗauke da maniyyata 418 daga ƙananan hukumomin Aliero, Koko/Besse, Bunza da Kalgo, tare da jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi.

Ya tabbatar wa maniyyatan da ingantattun tsare-tsaren jin daɗi, ciki har da samar da mafi kyawun masauki kusa da Masallacin Harami da ke Makka, abinci mai kyau da kuma biya musu Hadaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa na da ƙudirin tabbatar da jin daɗi da kare mutuncin dukkan alhazai.

Gwamna Idris ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ci gaba da al’adar tallafawa alhazai ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ɗaukar nauyin Hadaya, da kuma samar da sufuri kyauta domin gudanar da Ziyarah a Madina.

Yayin da ya yi kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka wa alhazai daga yankunansu, ya kuma buƙaci maniyyatan su sadaukar da kansu ga addu’o’i domin Jihar Kebbi da Najeriya, musamman a filin Arafat.

Tun da farko, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Musa Enabo, ya yaba wa Gwamnan bisa irin goyon bayan da yake bai wa alhazai. Ya bayyana muhimman matakan da aka ɗauka kamar biyan kuɗin Hadaya, inganta tsarin abinci da kuma samar da masauki mai inganci a Makka.

A jawabansu daban-daban, Malam Lawal Baiti Mai Kwalta da Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo sun yi wa’azi kan wajibcin aikin Hajji tare da jan hankalin maniyyata da su kiyaye ladabi, gaskiya da sadaukarwa a duk tsawon aikin ibadar.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara