Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Taya ‘Yan Wasan Najeriya Murnar Lashe Gasar Kakowa ta Afirka

Published

on

Daga Bello Wakili

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Najeriya  murna kan bajintar da ta nuna a Gasar Kokawa ta Afirka ta shekarar 2026 da aka gudanar a Alexandria, ƙasar Masar, inda ƙasar ta lashe kambun nahiyar karo na 15 a rukunin mata.

Shugaban ya bayyana nasarar a matsayin alamar daidaito, jajircewa da kuma abin alfahari ga ƙasa, yana mai cewa ‘yan kokawar Najeriya sun sake nuna dalilin da ya sa suke kan gaba a nahiyar Afirka.

Tinubu ya ce, ‘yan wasan wadanda suka sami lambar zinare 8 da azurfa 2 daga wasanni 10 a rukunin mata, tare da jimillar lambobin yabo 9 na zinare, 4 na azurfa da 3 na tagulla a dukkan rukuni, sun nuna ƙwarewa a matakin koli da kuma jajircewa a dukkan sassan tawagar.

Ya yaba da rawar da Mercy Genesis, Adijat Idris, Esther Asaolu da Mercy Adekuoroye suka taka, inda ya ce sun nuna ƙwarewa tare da nutsuwa.

Shugaban ya kuma yabawa Harrison Onovwiomogbhwo kan nasarar da ya samu a rukunin maza na freestyle.

Ya kuma jinjina wa gudunmawar Ebierelayefa Andrew, Stephen Akintewe, Dideikemei Erefagha, Solomon Ulabo da Saviour Egoli, yana mai cewa an sami nasara ne bisa hadin kan da suka nuna.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa wannan nasara na nuna sauyi a harkar wasanni a Najeriya, inda aka fara mai da hankali kan tsari, shirye-shirye da kuma bunƙasa ‘yan wasa na dogon lokaci.

Ya ce aikin Hukumar Wasanni ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Mallam Shehu Dikko, Bukola Olopade da tawagarsu tare da ƙungiyoyi da masu horaswa na fara ɗaukar ƙarfi ta hanyar tsarin da ke ƙarfafa da’a, daidaito da kuma ƙwarewa.

Shugaban ya ƙara da cewa nasarar da aka samu a Alexandria na nuna akwai sabbin ‘yan wasa da ake shiryawa domin su yi fice a manyan wasanni a nan gaba.

 

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai8 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara