Kasuwanci
Gwamna Nasir Ya Kaddamar da Sabuwar Kasuwar Kayan Gwari a Birnin Kebbi
Daga Sani Dutsinma
Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya kaddamar da sabuwar kasuwar kayan lambu ta zamani da aka gina a Birnin Kebbi, domin cika alkawarin da ya dauka tun da dadewa ga ‘yan kasuwa da mazauna yankin.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Idris ya tuna da yadda kasuwar take a baya, inda ya bayyana cewa wuri ne a bude kuma bai dace da harkokin kasuwanci ba.

Ya bayyana cewa shawarar sake gina kasuwar ta biyo bayan kiran da ‘yan kasuwar suka yi, wadanda suka nemi gwamnati ta taimaka musu da samar da muhalli mai kyau domin gudanar da kasuwancinsu.
Gwamnan ya ce an gina sabuwar kasuwar ce domin inganta rayuwar ‘yan kasuwa, musamman masu sayar da kayan ganye da sauran kayan abinci, ta hanyar samar musu da tsari mai kyau da kuma rumfunan da za su iya ajiye kayayyakinsu cikin cikin tsafta tare da gudanar da kasuwanci ba tare da tangarda ba.

Ya jaddada cewa aikin yana nuna kudurin gwamnatinsa na tallafawa harkokin tattalin arziki a matakin kasa da kasa, tare da tabbatar da cewa jama’a na cin gajiyar ayyukan gwamnati kai tsaye. Gwamna Idris ya kuma gode wa Allah bisa nasarar kammala aikin, sannan ya kaddamar da kasuwar domin amfanin jama’a.

A nasa jawabin, Shugaban Kasuwar Kayan Gwari, Umarun Basiru, ya nuna godiya ga gwamnan bisa cika alkawarinsa, inda ya bayyana ci gaban a matsayin babban abin da zai kara bunkasa rayuwar ‘yan kasuwa, tare da cewa sabuwar kasuwar za ta taimaka matuka wajen kara kudaden shiga ga jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
