Connect with us

Labarai

Kashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya

Published

on

Daga Bello Wakili 

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya kaddamar da jigilar maniyyata Hajjin 2026, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kashim Shettima  ya buƙaci maniyyatan da su nuna halaye nagari da za su ɗaukaka martabar Najeriya yayin zamansu a kasar Saudiyya.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya bayyana maniyyatan a matsayin jakadun Najeriya, ya yi kira a gare su da su nuna ladabi, tawali’u, haƙuri da gaskiya a duk tsawon aikin ibadar.

Ya ce aikin Hajji muhimmiyar alaka ce mai tsarki tsakanin gwamnati da al’umma, yana mai jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da tsaro, mutunci da jin daɗin dukkan maniyyata.

Jirgin farko ya ɗauki kimanin maniyyata 500 daga Jihar Kogi zuwa ƙasar Saudiyya, yayin da ake sa ran kusan ‘yan Najeriya 50,000 za su halarci aikin Hajjin bana.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci masu kula da harkokin Hajji, da masu aikin jiragen sama, da ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro, da su tabbatar da kyakkyawan haɗin kai da ingantaccen aiki yayin gudanarda shirin.

Shi ma da yake jawabi, Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya buƙaci maniyyatan da su yi addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da ƙoƙarin inganta jin daɗin maniyyata tare da aiwatar da gyare-gyare don inganta harkokin Hajji.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara