Labarai
Jihar Jigawa ta Kafa Kwamitoci na Musamman Don Inganta Walwalar Alhazai
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhaza ta Jihar Jigawa ta gudanar da taro da jami’anta na shiyyoyi da rukunin ma’aikata a ofishinta dake Birnin Makkah.
Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a zantawarsa da Wakilinmu Usman Mohammed Zaria dake Makka.
Yayi bayyanin cewar, makasudin gudanar da taron shine domin su kara jajircewa da kula da Alhazai a kasa mai tsarki.
Ya ce akwai kwamitoci da hukumar ta kaddamar wadda dukkan masu ruwa da tsaki suke ciki don samun bayanai na kullum-kullum da za su rika baiwa hukumar bayanai game da halin da Alhazan suke ciki, musamman dangane da abincin da ake basu tare da yawansa gami da ingancin abincin.
Game da batun lafiya kuwa, Alhaji Ahmed Labbo yace hukumar ta nusar dasu bisa bibiyar lafiyar Alhazai duk da anzo da likitoci kuma an raba su har Kashi biyu, tare da samar da isassun magunguna da tsarin kai su asibitoci har na kasar Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.
Yana mai nuni da cewar Alhazan jihar a zancen da ake yi yanzu suna cikin koshin lafiya.
Kazalika, Darekta Janar din ya bayyana cewar ya bada umarnin dukkan jami’an su saka layin wayar kasar Saudiyya domin samun saukin tuntubar juna akan tafiyar da aikin su cikin sauki, duba da yadda layin Najeriya akan fuskanci matsala wajen kiran waya.
Har ila yau, Labbo ya kuma ce za a basu kudin katin wayan da zasu rika tuntubar juna da bada bayanai domin cimma burin da aka sa a gaba.
Yana mai kara jan hankalin maniyyatan da su dukufa wajen ci gaba da gudanar da Salloli a masallacin Harami, duba da yadda aka kama masu masukai a kusa da Harami.
Yace su ci gaba da yiwa kananan hukumomin su da Jihar Jigawa da Najeriya addu’oi a yayin zaman su a kasa mai tsarki.
Ya yaba da yadda suke bin dokoki da ka’idojin da hukumomin kasar Saudi Arabia ta giindaya a bana.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
