Connect with us

Labarai

Cibiyar Kukah Ta Gabatar Da Tsare-Tsaren Karfafa Tsaron Al’umma

Published

on

Cibiyar Kukah Centre for Faith, Leadership and Public Policy ta gabatar da shawarwari da za su taimaka wa gwamnatoci a matakin jiha da tarayya wajen kafa ingantaccen tsarin doka da zai jagoranci jami’an tsaron al’umma domin inganta aikin su.

A yayin wani taro na gabatar da sakamakon bincike kan yadda ake samun rarrabuwar kai a harkar tsaron al’umma, Manajan aikin cibiyar, Terseer Bamber, ya ce an gudanar da binciken ne domin ƙarfafa tsarin doka da hukumomi wajen tabbatar da kyakkyawan aiki a fannin tsaro.

Ya ce binciken ya samu goyon bayan shirin Strengthening Peace and Resilience in Nigeria (SPRiNG) tare da haɗin gwiwar UK International Development, Tetra Tech, da Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Bamber ya ce bukatar wannan bincike ta taso ne sakamakon karuwar dogaro da ƙungiyoyin tsaron al’umma a Najeriya, musamman saboda matsalolin tsaro da rikice-rikicen kabilanci da addini a jihohi irin su Sokoto, Kaduna, Katsina, Benue da Plateau.

Ya nuna damuwa cewa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi ba su da tsayayyen tsarin aiki, lamarin da ke haifar da zargin cin zarafi da take haƙƙin ɗan Adam.

Shi ma shugaban tawagar binciken kuma shugaban Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Usman Abdulkadir, ya ce rahoton binciken mai shafuka 145 ya gano tushen da ya haddasa rarrabuwar kai a cikin tsarin tsaron al’umma.

Ya ce rahoton ya kuma bayar da shawarwari guda tara da za su taimaka wajen tsara yadda ake kafawa da gudanar da waɗannan ƙungiyoyi.

Farfesa Usman ya ce idan gwamnati ta amince da shawarwarin tare da kafa doka a kansu, hakan zai taimaka wajen hana siyasantar da tsaron al’umma musamman gabanin zaɓen shekarar 2027.

Taron ya samu halartar hukumomin gwamnati, shugabannin gargajiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Nasiru Muhamad/Sakkwato

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara