Labarai
Rashin Aikin Yi Ne Tushen Laifuka’ — Usman Dantata
Wani ɗan takarar siyasa daga Chanchaga a jihar Neja, Usman Shehu Isa wanda aka fi sani da Usman Dantata, ya ce samar wa matasa ayyukan yi ne zai zama babban abin da zai fi bai wa muhimmanci idan aka ba shi dama.
Ya bayyana cewa rashin aikin yi da zaman kashe wando na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa laifuka kamar sata da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a cikin al’umma.
Usman Dantata ya kuma gargaɗi matasa da su guji shiga harkokin daba da tashin hankali musamman a lokacin zaɓe, yana mai cewa ya kamata su zaɓi shugabannin da za su kare muradunsu maimakon karɓar kuɗi domin tayar da rikici.
Ya ƙara da cewa zai haɗa gwiwa da hukumomin tsaro wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci da garkuwa da mutane a jihar Neja.
‘Yar takarar kujerar Sanata ta jam’iyyar ADC daga jihar Katsina, Hajiya Amina Lawal Rafindadi, ta ce za ta mayar da hankali wajen samar da hanyoyin makamashi na daban domin bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Katsina ta Tsakiya.
Ta bayyana hakan ne bayan miƙa takardun tsayawa takararta a ofishin jam’iyyar ADC da ke Abuja.
A cewarta, babu wata al’umma da za ta samu cikakken ci gaba ba tare da wadataccen makamashi ba.
Hajiya Amina ta ce maimakon ci gaba da dogaro da wutar lantarki ta ƙasa, ya kamata a samar da tashoshin hasken rana a kowace ƙaramar hukuma domin ƙara yawan aiki da bunƙasa tattalin arziki.
Ta kuma ce idan aka zaɓe ta, za ta samar da shirye-shiryen da za su ƙarfafa mata da matasa ta fuskar tattalin arziki.
Wata ‘yar takarar kujerar majalisar wakilai daga Shanga/Yauri a jihar Kebbi, Hajiya Asia Aminu, ta buƙaci mata su haɗa kai su mara wa junansu baya a harkokin siyasa.
Ta ce matan Najeriya yanzu sun fahimci muhimmancin shiga siyasa kuma suna shirye su goyi bayan mata ‘yan uwansu.
A cewarta, tun daga jamhuriya ta biyu maza ne suka mamaye harkokin siyasa duk da irin gudunmawar da mata ke bayarwa musamman a lokutan zaɓe.
Bashir Mayere/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
