Labarai
ADC Kebbi Ta Koka Kan Tsare Mambobinta
Jam’iyyar ADC reshen Jihar Kebbi ta bayyana damuwa kan abin da ta kira kamawa da tsare mambobinta ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na jihar.
Sakataren jam’iyyar a jihar, Abubakar Bawa Kalgo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Birnin Kebbi.
Kalgo ya zargi wasu jami’an gwamnatin Jihar Kebbi da amfani da bangaren shari’a da wasu hukumomin gwamnati wajen tauye dimokuradiyya da kuma danniya ga jam’iyyun adawa, inda ya yi kira ga hukumar kula da shari’a ta kasa National Judicial Council da Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kebbi da su shiga lamarin.
Ya ce jam’iyyar ADC a Kebbi na kira ga gwamnatin jihar da bangaren shari’a da su mutunta doka, adalci da kuma ka’idojin dimokuradiyya.
A cewarsa, shugaban jam’iyyar na jihar, Injiniya Sufiyanu Bala, wanda ya samu nasara bayan gudanar da zabukan cikin gida, jami’an ‘Yansanda sun kama shi bisa sammacin da Kotun Majistare ta Farko da ke Birnin Kebbi ta bayar.
Kalgo ya kara da cewa an yi yunkurin gurfanar da shi a gaban wannan kotu sau da dama, amma abin bai yiwu ba saboda wasu kura-kurai na tsari da doka.
Ya bayyana cewa duk da haka, ’yan sanda sun ci gaba da shirin gurfanar da shi bisa nacewar kotun, inda lauyan wanda ake zargin, Barrista A.A. Fingilla, ya bukaci alkalin kotun ya janye kansa daga shari’ar bisa zargin son rai, amma kotun ta yi watsi da bukatar, lamarin da ya sa lauyan ya fice daga kotun.
Sakataren jam’iyyar ya kuma bayar da misalan wasu mambobi da aka kama tare da tsare su, ciki har da Umar Abubakar wanda aka fi sani da Abu Yarima, wanda ya shafe kwanaki 25 a tsare bisa zargin yin kalaman siyasa a kafafen sada zumunta, da kuma Husaina Ahmed Jega, Nasiru Garba Hashim da Umar Yakubu Kamba da sauransu.
A cewarsa, jam’iyyar ta yanke shawarar gabatar da koke ga National Judicial Council, Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Kebbi, Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta duniya wato Amnesty International, da kuma Ma’aikatar Shari’a ta Amurka domin neman a tsoma baki tare da kare dimokuradiyyar Nijeriya daga abin da ya kira amfani da hukumomin gwamnati wajen cimma muradun siyasa.
Sai dai da yake mayar da martani, rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta musanta zargin tsare Injiniya Sufiyanu Bala ba bisa ka’ida ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa ana tsare da Sufiyanu Bala ne bisa sahihin umarnin kotu daga Kotun Majistare ta Birnin Kebbi, wanda ya umurci a tsare shi har zuwa ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da shari’a.
Sanarwar ta jaddada cewa tsarewar tasa ya biyo bayan umarnin kotu ne, ba wai kama shi barkatai ba daga rundunar ’yan sanda.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa a ranar da aka tsare shi, Injiniya Sufiyanu Bala ya bukaci kulawar lafiya, kuma nan take aka kai shi wani asibiti a Birnin Kebbi inda ake kula da lafiyarsa yadda ya kamata.
Dutsinma/Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
