Connect with us

Labarai

Dan Takarar Gwamnan Sokoto Na ADC Ya Tsalleke Rijiya da Baya Daga Yunkurin Hallaka Shi

Published

on

Daga Nasiru Muhammad, Sakkwato

Dan takarar gwamnan Jihar Sokoto na jam’iyyar  ADC, Hon Mannir Muhammad Dan’Iya, ya zargi jami’an rundunar tsaron da gwamnatin jihar ta kafa da kai hari kan ayarin motocinsa.

Da yake zantawa da manema labarai a Sokoto, dan takarar ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da yake dawowa daga raka Sanata Aminu Waziri Tambuwal zuwa filin jirgin sama domin komawarsa Abuja, bayan wasu harkokin siyasa da ya gudanar a Sokoto.

Dan’Iya ya ce harin ya faru ne a yankin filin jirgin saman Sokoto da misalin ƙarfe 9 na daren Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, Dan’Iya ya ce jami’an rundunonin tsaron jihar guda biyu sun tare ayarin motocinsa, tare da hana su wucewa, suna masu cewa umarni daga sama aka ba su na kada su bari mambobin ADC su shiga Sokoto.

Ya bayyana cewa ƙoƙarin jami’an tsaron da ke tare da shi na sasanta lamarin bai yi nasara ba, domin an harba bindigogi kan motarsa, sannan aka tsare jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) guda biyu da ke cikin tawagar tsaronsa.

Dan’Iya ya tabbatar da cewa da kansa ya kai ƙorafi ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sokoto, inda ya bayyana masa yadda lamarin ya faru tare da neman a yi masa adalci.

Yana mai cewa lamarin barazana ce kai tsaye ga rayuwarsa, duk da cewa ya kuɓuta ba tare da rauni ba, Dan’Iya ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike cikin gaggawa kuma cikin ’yanci ba tare da nuna son kai ba.

Ya kuma buƙaci a adana tare da bincikar dukkan hujjojin da ake da su, ciki har da faifan bidiyo, bayanan ayyukan jami’an tsaro, shaidun waɗanda suka ga abin da ya faru da kuma duk wani rahoto da ya shafi amfani da makamai.

Ya yi kira ga Kwamishinan ’Yan Sanda, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Darakta-Janar na DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike nan take tare da gano waɗanda suka bayar da umarnin, tantance jami’an da suka aikata ba daidai ba, tare da tabbatar da sakin jami’an DSS guda biyu cikin gaggawa idan har yanzu suna tsare.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai24 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara