Connect with us

Labarai

Shugaban Majalisar Wakilai Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Ilimi, Lafiya Da Tsaro Ga Al’umma

Published

on

Daga Ibrahim Suleiman, Zaria

Shugaban Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Dakta Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa manufar shugabanci ita ce biyan muhimman buƙatun al’umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da tsaron jama’a.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, yayin bikin aza harsashin ginin wasu ayyukan raya ƙasa da kuma ƙaddamar da wasu ayyukan mazabarsa.

A cewarsa, ya kamata kowane yaro da aka saka a makarantar firamare ta gwamnati ya samu aji mai kyau da zai ba shi damar karatu cikin yanayi mai dacewa. Haka kuma, duk macen da ta je neman magani a Chikaji ta samu damar gudanar da gwaje-gwajen lafiya ba tare da yin doguwar tafiya mai wahala ba, yayin da matasa a Bomo su samu damar koyon ilimi, rubuta jarabawa da samun takardun shaidar cancanta.

Ya ce ginin sabon rukunin ajujuwa guda goma, tare da ofisoshi da bandakuna a Makarantar Firamare ta Sa’idu, zai taimaka wajen samar wa yara ingantaccen yanayin karatu.

Abbas ya ƙara da cewa sabuwar makarantar sakandare, Cibiyar Karatu ta Jami’ar NOUN da kuma cibiyar rubuta jarabawar kwamfuta (CBT Centre) za su samar wa matasa damar ci gaba da karatu bayan firamare, tare da ba su damar yin gogayya da sauran matasa a wannan zamani na fasahar sadarwa.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 20 da cibiyar gwaje-gwajen lafiya na buƙatar samar musu da kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata, yana mai cewa ginin asibiti ba tare da ma’aikata ba, zai sa marasa lafiya su ci gaba da jiran samun kulawa.

Ya ƙara da cewa sabon ofishin ’yan sanda da hedikwatar rundunar yankin za su taimaka wajen gaggauta kai ɗauki, inda ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi bisa matakan da suke ɗauka wajen kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Abdulkadir Mu’azu Meyere, ya wakilta, ya yaba wa Shugaban Majalisar bisa jawo ayyukan ci gaba zuwa ƙananan hukumomi takwas na shiyyar Sanata ta Ɗaya. Ya kuma yi kira ga al’ummar Sabon Gari da su zaɓi ’yan takarar jam’iyyar APC daga sama har ƙasa.

Haka kuma, ɗan takarar Sanata na APC a Shiyyar Sanata ta Ɗaya, kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya buƙaci al’ummar Sabon Gari da su tabbatar da samun cikakkiyar nasara ga APC a zaɓuka masu zuwa.

Bikin aza harsashin gine-ginen ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC da sarakunan gargajiya da kuma dimbin magoya bayan jam’iyyar.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara