Labarai
Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.
Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar.
Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026.
Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.
A watan Maris 2025, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamna da majalisa wanda kusan ya jawo rugujewar tafiyar da mulki a jihar.
Shugaban ƙasa ya kuma tsige Gwamna Fubara, mataimakinsa da kuma dakatar da majalisar jihar.
Sai dai an dawo da gwamnan da ’yan majalisar a jihar bayan an ɗage dokar ta-bacin a watan Satumba, tare da fatan cewa zaman lafiya ya dawo tsakanin bangarorin biyu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
