Connect with us

Labarai

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Published

on

Daga Khadijah Aliyu 

Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Laraba, 11 ga Nuwamban 2026, domin nazari da tantancewa kafin amincewa da shi.

Shugaban Majalisar, Jibril Ismail-Falgore ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar, bayan karanta wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar, inda ya sanar da aniyarsa ta gabatar da daftarin kasafin kuɗin.

A cikin wasiƙar, Gwamna Yusuf ya ce gabatar da kasafin kuɗin ya zama wajibi a kansa bisa tanadin sashe na 121(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima.

Ya bayyana cewa daftarin kasafin kuɗin ya ƙunshi hasashen kuɗaɗen shiga da kashe kuɗaɗen jihar a shekarar kuɗi ta 2027, wanda zai miƙa wa ’yan majalisar domin nazari da amincewa da shi.

Gwamnan ya kuma buƙaci majalisar da ta shirya dukkan abubuwan da suka dace domin gudanar da zaman gabatar da kasafin kuɗin.

A wani labarin kuma, Majalisar ta amince da wani ƙuduri da ke kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta gyara Cibiyar Mata ta City Women’s Centre da kuma cibiyar Hukumar Ilimin Manyan Makarantu (Agency for Mass Education), da ke kan titin Fadar Sarki, Kofar Nassarawa, a Ƙaramar Hukumar Kano Municipal.

Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, Nabil Aliyu Daneji, ne ya gabatar da ƙudurin, inda ya ce cibiyoyin sun lalace sakamakon rashin kulawa na tsawon lokaci, lamarin da ya shafi ayyukan da suke gudanarwa ga mata da manyan ɗalibai.

Ya bayyana cewa ci gaba da lalacewar cibiyoyin na kawo cikas ga ƙoƙarin bunƙasa ilimi, koyon sana’o’i da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma.

Ɗan majalisar ya jaddada cewa gyara da inganta cibiyoyin zai dawo da su cikin yanayin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Bayan muhawara, Majalisar ta amince da ƙudurin tare da kira ga gwamnatin jihar da ta ba da fifiko wajen yin cikakken gyara da inganta cibiyoyin.

Majalisar ta bayyana cewa dawo da cibiyoyin cikin yanayin aiki zai inganta damar samun ilimi, koyon sana’o’i da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki, musamman ga mata da manyan ɗalibai.

Fassara: Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara