Labarai
Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna ne wuri guda domin ƙarfafa haɗin kai da samar da tsari guda da jam’iyyar APC za ta yi amfani da shi wajen yaƙin neman zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jigawa na 2027 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse, inda aka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Namadi.
Namadi ya bayyana gamsuwarsa da yawan mutanen da suka halarci taron, yana mai cewa hakan ya nuna ƙarfin jam’iyyar APC da ci gaba da kasancewar ta a faɗin jihar.
Ya ce taron ya ƙara masa kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC a shirye take ta samu nasara a dukkan matakan zaɓen da ke tafe.
Gwamnan ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta su haɗa kai domin ganin an sake zaɓen Shugaba Tinubu da shi a matsayin gwamna, tare da zaɓen ’yan takarar APC zuwa Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.
Namadi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, da yardar Allah, jam’iyyar za ta samu nasara a dukkan zaɓukan.
Haka kuma, ya bayyana cewa Jihar Jigawa a shirye take ta cika burin samar wa Shugaba Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Gwamnan ya ce yawan mutanen da suka halarci taron ƙaddamar da kwamitin ya ƙara masa kwarin gwiwar cewa jihar za ta cimma wannan buri.
Kaddamar da kwamitin ya haɗa manyan shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa ƙarƙashin tsari guda, domin tsara ayyukan wayar da kan masu zaɓe da tattara goyon baya ga Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi gabanin babban zaɓen 2027.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Namadi ne shugaban kwamitin, yayin da aka naɗa Alhaji Lawan Ya’u Roni a matsayin Darakta-Janar.
Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman; tsohon Gwamna, Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu; tsohon Gwamna, Sanata Ibrahim Saminu Turaki; da Shugaban APC na jihar, Alhaji Ahmad Garba MK, su ne mataimakan shugaban kwamitin.
Sauran manyan jami’an kwamitin sun haɗa da Sanata Muhammad Ibrahim da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakan shugabanni na Arewa maso Gabas na ɗaya da na biyu.
Haka kuma, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin da Alhaji Farouk Adamu Aliyu su ne mataimakan shugabanni na Kudu maso Yamma na ɗaya da na biyu, yayin da Alhaji Isa Gerawa da Hajiya Rabi Ishaq za su kula da Arewa maso Yamma na ɗaya da na biyu.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai1 day agoArewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari
