Connect with us

Labarai

Tsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Tsoffin Gwamnonin Jihar Jigawa sun yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa nasarorin da ya samu wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma cikin ƙasa da shekaru huɗu da fara mulkinsa.

Tsofaffin Gwamnonin, Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu da Sanata Ibrahim Saminu Turaki, sun bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jigawa na 2027 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse, inda aka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Namadi gabanin zaɓe mai zuwa.

Tsoffin gwamnonin sun bayyana kwarin gwiwar cewa nasarorin gwamnatin Namadi za su zama babban makamin yaƙin neman zaɓe, tare da ƙara wa jam’iyyar APC damar samun nasara a zaɓen 2027.

Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu ya bayyana Gwamna Namadi a matsayin shugaba mai gaskiya da riƙon amana, yana mai cewa ayyukan gwamnatinsa ba su bar wani gurbi na suka ba.

Ya ce gwamnan ya nuna gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, yana mai cewa yawancin masu sukar sa suna yin hakan ne saboda hassada da bambancin siyasa.

A nasa ɓangaren, Sanata Ibrahim Saminu Turaki ya bayyana Namadi a matsayin shugaba mai adalci, tsayayyen ra’ayi da tausayi, wanda ya samu gagarumar nasara a fannin samar da ababen more rayuwa da ilimi.

Ya yaba musamman kan ayyukan hanyoyi da gwamnatin ke gudanarwa a faɗin jihar, da kuma ɗaukar dubban malamai aiki, yana mai cewa ba a taɓa samun irin wannan ɗaukar malamai ba tun bayan barinsa mulki.

Turaki ya ce a baya wasu makarantu sun fuskanci barazanar rufewa saboda ƙarancin malamai, sai gashi gwamnatin mai ci yanzu ta magance matsalar ta hanyar ɗaukar malamai da dama aiki.

Fassara: Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara