Labarai
Jigawa: Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kafa Kwamitin Tantance Bayanan Maniyyatan 2027
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai tattara, tare da yin nazari da kuma tantance bayanan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2027.
Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
Ya jaddada muhimmancin tattara sahihan bayanai da tantance su domin tabbatar da ingantaccen shiri da kuma gudanar da aikin Hajjin cikin tsari.
Alhaji Labbo ya bayyana cewa jami’an gudanarwa uku na hukumar ne za su jagoranci aikin kwamitin, waɗanda suka haɗa da Daraktan Ayyuka, Alhaji Muhammad Garba; Daraktan Gudanarwa da Kuɗi, Alhaji Mohammed Umar Sambo; da Babban Akanta, Alhaji Muntari Mohammed.
Ya ƙara da cewa dukkan shugabannin shiyyoyin hukumar da mataimakansu a faɗin jihar za su kasance mambobin kwamitin, domin tabbatar da kyakkyawan haɗin gwiwa da tantance bayanan maniyyata yadda ya kamata.
Daraktan Janar ɗin ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin muhimman matakan shirye-shiryen Hajji, musamman ganin cewa ana sa ran fara aikin bayar da biza nan ba da jimawa ba.
Ya buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu bisa ƙwazo da gaskiya, tare da tabbatar da cewa an tattara dukkan bayanan da ake buƙata kuma an tantance su yadda ya kamata.
Alhaji Labbo ya bayyana cewa hukumar ta kammala kusan kashi 40 cikin 100 na shirye-shiryen aikin Hajjin 2027, tare da cewa yana da yakinin za a kammala sauran ayyukan bisa jadawalin da aka tsara.
Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta fitar da jadawalin wayar da kan maniyyata da kuma shirye-shiryen horas da su nan ba da jimawa ba, a dukkan shiyyoyi da ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Daraktan Janar ɗin ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa ci gaba da tallafa wa hukumar da kuma jajircewarsa wajen kula da jin daɗin Alhazai a jihar.
Ya sake jaddada aniyar hukumar na tabbatar da ingantaccen shiri, kyakkyawan tsari da kuma inganta ayyukan hidima ga maniyyata aikin Hajjin 2027.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
