Labarai
Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.
Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.
Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.
Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”
A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.
Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.
Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.
Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.
Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
