Labarai
PDP ta Sallami Wike, Fayose, Anyanwu da Wasu Mutane
Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu.
PDP ta yanke wannan hukunci ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu, Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, sannan Samaila Burga, shugaban PDP na Jihar Bauchi, ya mara masa baya.
A baya, bangaren jam’iyyar da ke goyon bayan Wike sun kai ƙara kotu don a hana gudanar da taron.
Amma PDP ta samu hukuncin da ya ba ta damar ci gaba da taron daga Kotun Ƙoli ta Jihar Oyo.
Kwana biyu kafin taron, Mao Ohuabunwa, Shugaban Majalisar Amintattu (BoT) na ɓangaren Wike, ya ce duk wanda ya tafi Ibadan don taron hutu ya je yi, domin doka ba za ta aminta da shi ba.
A cewarsa, Anyanwu ya riga ya fitar da sanarwar ɗage taron.
Ohuabunwa ya ce: “Mun zauna a matsayin kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP, muka duba abubuwan da muka yi. Mun yadda da bin hukuncin kotu game da taron Ibadan. Don haka ba mu da hannu a taron.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
