Labarai
Gwamna Kefas na Taraba ya shirya Barin PDP Zuwa APC
Gwamnan jihar Taraba ya sanar da cewa zai fice daga jam’iyyar PDP mai adawa zuwa All Progressives Congress (APC) ranar Laraba mai zuwa.
Da yake magana yayin wata ziyara a filin wasa na Jolly Nyame ranar Asabar – inda nan ne wurin taron komawa APC din – Gwamna Agbu Kefas ya ce matakin komawa APC ɗin yana da alaƙa ne da ciyar da rayuwar mazauna Taraba, ba wai raɗin kansa ba.
“Zan fita daga PDP zuwa APC ranar 19 ga watan Nuwamba a hukumance,” in ji shi.
“Wannan yunƙuri magana ce ta makomar al’ummar Taraba kuma mutane da yawa za su halarci bikin.”
Da ma gwamnan na cikin waɗanda ba su halaraci babban taron PDP na ƙasa da aka gudanar a birnin Ibadan ba ranar Asabar, inda ta zaɓi sababbin shugabanni.
Sauran su ne Gwamnan Rivers Fubara da Adeleke na jihar Osun.
Idan gwamnan ya fita daga jam’iyyar zai zama jihohin da PDP ke mulki sun koma takwas kenan, yayin da a baya-bayan nan gwamnonin Bayelsa da Delta suka koma APC ta Shugaba Tinubu mai mulki.
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
-
Labarai2 days agoJihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki
-
Kasuwanci2 days agoBOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
-
Labarai5 days agoKashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya
-
Labarai4 days agoGwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
-
Labarai2 days agoGwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida
-
Ilimi2 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
