Labarai
APC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Gwani na Sanatoci a Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta sanar da waɗanda suka yi nasara a zaɓen fidda gwani na sanatoci a yankuna uku na jihar, inda ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana.
A Zamfara ta Tsakiya, Ikra Aliyu Bilbis ta yi nasara da ƙuri’u 127,686, yayin da a Zamfara ta Yamma Abdulaziz Yari ya lashe zaɓen da ƙuri’u 125,235.
Haka kuma a Zamfara ta Arewa, Sahabi Alhaji Yau ya zama zakara bayan samun ƙuri’u 65,642.

Shugaban kwamitin zaɓen, Farfesa Bala Ishaq, ya ce ba a samu tashin hankali ko wata babbar matsala ba yayin gudanar da zaɓen.
Ya kuma buƙaci dukkan masu ƙorafi su miƙa koke-kokensu ga kwamitin ɗaukaka ƙara na jam’iyyar, wanda zai fara zama daga ranar 28 ga watan Mayun 2026.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
