Connect with us

Labarai

INEC Za Ta yi Zaben Cike Gurbi na Dawakin Kudu/Warawa Ranar 20 ga Watan Yuni

Published

on

Daga Khadijah Aliyu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta bayyana ranar 20 ga watan  Yunin 2026 domin gudanar da zaɓen cike gurbi na kujerar Warawa/Dawakin Kudu a Jihar Kano bayan rasuwar ɗan majalisar wakilai.

Kwamishinan Zabe na Jihar (REC), Zango Abdu, ya ce an riga an fara shirin zaɓen, inda aka kai ziyara domin duba matakin shiri a ƙananan hukumomin Warawa da Dawakin Kudu.

Ya bayyana cewa Warawa na da rumfunan zaɓe 303 da masu rajista 162,445, yayin da Dawakin Kudu ke da  rumfunan zaɓe 143 da masu rajista 75,623

INEC ta ce fiye da ma’aikata 2,000 ne za a tura domin gudanar da aikin, tare da haɗin gwiwar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC,  da jami’an tsaro don tabbatar da zaɓe lami lafiya.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa Kano na kan gaba a rajistar sabbin masu kaɗa ƙuri’a, inda fiye da mutum 210,000 suka yi rajista, kuma sama da 190,000 sun kammala cikakken rajista.

REC ya roƙi ‘yan siyasa da su guji tashin hankali, yana mai cewa ana bukatar zaman lafiya domin sahihin zaɓe mai inganci.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara