Connect with us

Labarai

Kano: Hukumar Hisbah Ta yi Karin Girma ga Kwamandojin Kananan Hukumomi

Published

on

Daga Khadijah Aliyu 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa kwamandojinta na Kananan Hukumomin jihar 44 karin matsayi a wani biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar.

Da yake jawabi yayin bikin karin matsayi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Aminu Daurawa, ya bayyana cewa an yi karin matsayin ne bisa la’akari da jajircewa, himma da kuma kwazon jami’an wajen gudanar da ayyukansu.

Daurawa ya bukaci kwamandojin da aka yi wa karin matsayi su kara kaimi tare da inganta ayyukansu domin tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar wannan karin matsayi.

Jami’an da a baya suke da mukamin Mataimakan Sufuritanda (Assistant Superintendents), an daga su zuwa mukamin Sufuritandan Hisbah (Hisbah Superintendents).

Babban Kwamandan ya kuma shawarci jami’an da aka yi wa karin matsayin da su kasance masu nuna kwarewa da hakuri yayin gudanar da ayyukansu, tare da guje wa duk wani abu da ka iya bata martaba ko mutuncin hukumar.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka yi wa karin matsayi, Hamidan Tanko, wanda shi ne Kwamandan Karamar Hukumar Municipal kuma Shugaban Dandalin Kwamandojin Hisbah na Kananan Hukumomi 44, ya nuna godiya ga shugabannin hukumar bisa wannan karin matsayi.

Ya bayyana karin matsayin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma ya dace, tare da kira ga abokan aikinsa da su ci gaba da nuna gaskiya, aiki tukuru, rikon amana da sadaukarwa wajen gudanar da aiki.

Daga cikin wadanda suka taimaka wa Babban Kwamandan wajen bikin sanya sabbin mukamai akwai Mukaddashin Babban Kwamanda Mujahid Aminuddeen Abubakar, Khadija Sagir Suleman da sauran manyan jami’an hukumar.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara