Connect with us

Ilimi

Kwamishinan Kananan Hukumomi A Katsina Ya Gina Da Gyaran Azuzuwa A Makarantar Islamiyya Ta Dutsin-Ma

Published

on

 

Daga Adamu Yusuf

 

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Katsina, Alhaji Bashir Tanimu Gambo Dutsin-Ma, ya gina sabbin azuzuwa guda uku tare da gyaran wasu guda uku a makarantar Abdullahi Bin Abbas Islamiyya da ke karamar hukumar Dutsin-Ma, a wani bangare na kokarinsa na bunkasa ilimin addinin Musulunci da cigaban al’umma.

 

An kaddamar da aikin ne a gaban malamai na addinin Musulunci, shugabannin gargajiya, masu ruwa da tsaki na al’umma da mazauna yankuna daban-daban na karamar hukumar.

 

Mazauna yankin sun bayyana wannan aiki a matsayin babban gudunmawa wajen inganta yanayin koyarwa da koyo ga dalibai da malamai, tare da karfafa ilimin addini a cikin al’umma.

 

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Bashir Tanimu Gambo Dutsin-Ma, wanda mutane da dama ke kira da “Khadimul Islam” sakamakon yadda yake tallafawa harkokin addini da ayyukan jin kai, ya samu yabo kan jajircewarsa wajen bunkasa ilimi da cigaban karkara a fadin Jihar Katsina.

 

A jawabinsa yayin bikin kaddamar da aikin, Kwamishinan ya sake jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafawa cibiyoyin addini da ilimi, yana mai cewa zuba jari a bangaren ilimi yana da matukar muhimmanci wajen cigaban al’umma da kyautata tarbiyya.

 

Ya kuma bayyana cewa ana shirin gyaran bangaren sama na ginin makarantar cikin watanni biyu masu zuwa.

 

A cewarsa, za a mayar da ginin da aka gyara ofishin kungiyar IZA a Dutsin-Ma domin kara habaka ayyukan addini da ilimi a yankin.

 

Taron ya samu halartar manyan malamai, limamai, sarakunan gargajiya, shugabannin matasa da sauran al’umma, wadanda suka gudanar da addu’o’i na musamman ga Kwamishinan, suna rokon Allah Ya saka masa da alheri tare da ba shi nasara wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima.

 

Mazauna yankin sun kuma nuna jin dadinsu kan aikin, suna bayyana shi a matsayin taimako mai muhimmanci da zai amfani al’ummomi masu zuwa a Dutsin-Ma da kewaye.

Labarai

Labarai19 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai1 day ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai1 day ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai1 day ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai1 day ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara