Labarai
Bikin Sallah: Sarkin Kauru Ya Gargaɗi Matasa Kan Daba da Siyasar Ƙiyayya
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Sarkin Kauru, Mai Martaba Zakari Ya’u na Biyu, ya yi kira ga al’ummar masarautarsa da ke Jihar Kaduna da su rungumi zaman lafiya, tare da sa ido kan harkokin tsaro da kuma taka rawar gani wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na ci gaban al’umma.
Sarkin ya yi wannan kira ne a cikin saƙon sa na Babbar Sallah da ta gudana a ranar Laraba, 10 ga watan Zul-Hijjah shekarar 1446 bayan Hijira.
Zakari Ya’u na Biyu ya buƙaci jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen tallafa wa jami’an tsaro duk da cewa zaman lafiya ke ci gaba da dawowa a yankin, yana mai jaddada cewa tsaro alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara ƙaimi wajen tarbiyantar da ’ya’yansu muhimmancin zaman lafiya da kyawawan ɗabi’u, yana mai bayyana cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma.
Dangane da harkokin lafiya kuwa, Sarkin ya shawarci jama’a da su kula da tsaftar jiki da ta muhalli, sannan su nemi kulawar likitoci cikin gaggawa idan suka kamu da rashin lafiya.
Hakazalika, ya ƙarfafa wa mata masu juna biyu gwiwar zuwa awo a asibiti, tare da kira ga jama’a da su rungumi shirye-shiryen rigakafi.
Mai martaban ya kuma jaddada muhimmancin yin rajistar haihuwa da mutuwa, yin katin shaidan dan ƙasa da kuma rajistar katin zaɓe, yana mai cewa samun sahihan bayanan yawan jama’a zai taimaka wa gwamnati wajen samar da ayyukan ci gaba da more rayuwa.
Da yake magana kan harkokin siyasa, Sarkin ya gargaɗi matasa da su guji daba da siyasar ƙiyayya, yana mai kira gare su da su rungumi siyasa cikin lumana tare da mutunta ra’ayoyin juna.
Ya kuma ƙarfafa wa masu kaɗa ƙuri’a gwiwar yin zaɓe cikin lumana a nan gaba, yana mai cewa kaɗa ƙuri’a hakki ne da kundin tsarin mulki ya bayar, kuma hanya ce ta samar da shugabanci nagari.
Dangane da rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake yawan samu, Zakari Ya’u na Biyu ya gargaɗi ɓangarorin biyu da su guji duk wani abu da zai iya haddasa rikici.
Ya buƙaci manoma da su mutunta hanyoyin shanu, sannan ya yi kira ga makiyaya da su kula da dabbobinsu yadda ya kamata domin kauce wa lalata gonaki.
Sarkin ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu wajen aikata barna zai fuskanci hukunci, yana mai jaddada cewa Majalisar Masarautar Kauru ta himmatu wajen hana rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani bisa ayyukan ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Kauru.
Zakari Ya’u na Biyu ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta tallafa wa manoma da taki, magungunan kashe ƙwari da ingantattun iri, tare da cika alƙawarin samar da wutar lantarki ga yankin da kuma gina muhimman hanyoyi a garin Kauru da kewaye.

Mallam Muhammad Sani Suleiman (Danburam Kauru)
Da yake jawabi, Sakataren Masarautar, Muhammad Sani Suleiman (Danburam), ya ce Sarkin ya yaba wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Kauru, Bashir Tanko Dawaki, bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban yankin.
Danburam Kauru ya kuma yi fatan Allah Ya sa a cigaba da bukukuwan Sallah lafiya tare da karɓar ibadun al’ummar Musulmi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
