Connect with us

Labarai

Arfa: Farfesa Birnin Kudu Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’a ga Najeriya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Farfesa Abubakar Sani Birnin Kudu, ya yi kira ga Alhazan Najeriya da su yi amfani da sa’o’i masu albarka na ranar Arfa wajen yin addu’o’i masu yawa domin ƙasar nan.

Ya yi wannan kira ne a cikin hudubarsa ga Alhazan Jihar Jigawa a tantunansu da ke filin Arfa a ƙasar Saudiyya.

Ya buƙace su da su nemi taimakon Allah domin samun zaman lafiya, shiriya ga shugabanni, da kuma kawo ƙarshen matsalolin talauci da rashin tsaro da suka addabi ƙasar, musamman matsalar ’yan bindiga a yankin Arewacin Najeriya.

Farfesa Abubakar Sani Birnin Kudu ya kuma bayyana cewa ranar tara ga watan Zul-Hijja ita ce ake kira ranar Arfa.

Ya nuna cewa a wannan rana ne Alhazai ke taruwa a Dutsen Arfa domin yin addu’a da roƙon Allah.

An yi imani cewa Annabi Muhammad (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta bankwana a Dutsen Arfa a lokacin Hajjin sa na ƙarshe.

A cikin hudubar, Annabi Muhammad (SAW) ya jaddada muhimman ƙa’idojin Musulunci da suka haɗa da daidaito, adalci, da mutunta rayuka da dukiyoyin mutane.

Haka kuma ya sake nanata muhimmancin bin Alƙur’ani da koyarwarsa a matsayin hanya zuwa ga shiriya da kyawawan ayyuka.

A wata hira da RediyonNajeriya, Ibrahim Abdullahi da Ibrahim Mukhtar sun bayyana cewa ranar Arfa rana ce mai cike da shauki da farin ciki.

Sun bayyana ranar a matsayin rana da kowane Musulmi ya kamata ya yi burin gani, ta hanyar cika rukunan Musulunci na gudanar da aikin Hajji aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

“Wannan ginshiƙi ne na addini, rana ce ta farin ciki da godiya. Ina jin ni mai albarka ne ƙwarai da gaske kasancewata cikin wannan tafiya ta ibada.”

Sa’adatu Mufeedah Aminu Sambo, wadda ke gudanar da Hajji a karon farko, ta bayyana matuƙar godiyarta ga Allah bisa damar da ta samu na shiga wannan tafiya mai albarka.

“Ina godiya ga Allah da Ya ƙaddara ni cikin waɗanda suka samu damar gudanar da Hajjin bana. Ina addu’ar Allah Ya karɓi ibadunmu da addu’o’inmu, kuma Ya ba wasu ma damar samun wannan tafiya ta ibada a nan gaba,” in ji Mufeedah.

Alhazan sun yi addu’ar Allah shiriya ga shugabannin Najeriya, Ya sanya tsoronSa a zukatansu, kuma Ya bai wa ƙasar zaman lafiya mai ɗorewa.

Usman Muhammed Zaria 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara