Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta bukaci Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
Shugaban Hukumar Alhazan Malam Salihu Abubakar ne ya yi kiran, yayin ziyarar aiki ga jami’an NAMA a filin jirgin sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduan.
Malam Salihu Abubakar, wanda sakataren gudanarwar hukumar Malam Baba Muhammad Rufa’i ya wakilta, ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar aikin Hajji akoda yaushe, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.
Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri, tare da yin kira ga hukumar ta NAMA, da ta tabbatar da samar da duk wasu kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.
A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabuwar hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin na aiki ne zuwa ƙarfe 5 na yamma.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da burin ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.
Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.
Rel/Adamu Yusuf
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
