Labarai
Hajj2026: Mahajjatan Jigawa Sun Shirya Zuwa Arfa Cike da Kwarin Gwiwa
Daga Usman Muhammad Zaria
Mahajjatan Jihar Jigawa sun fara gudanar da ibadun aikin Hajjin shekarar 2026 cikin kyakkyawan yanayi, yayin da ake jigilar su daga sansanin Mina zuwa filin Arafat.
Aikin Hajji kan fara ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Zul-Hijja a kowace shekara, inda ake fara kai mahajjata zuwa sansanin Mina, sannan daga bisani su wuce Arafat, Muzdalifa, da Jamaratul Akaba, sannan su koma Makka domin domin yin Dawaful Ifadha.
Yawancin mahajjatan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun bayyana cewa duk da wahalhalun da ke tattare da gudanar da ibadun Hajji, suna da ƙwarin gwiwar gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.
Wasu mahajjata daga ƙananan hukumomin Kirikasamma da Jahun, Alhaji Musa Yau Muhammad da Alhaji Sabitu Hussaini, sun bayyana cewa tsoron Allah da ƙaunarsa ne ke ba su ƙarfi da juriyar fuskantar wahalhalun Hajji, domin Allah Ya yi alƙawarin amsa addu’o’in bayinsa. Sun ce wajibi ne su jure wahalhalun saboda babu abin alheri da ke zuwa cikin sauƙi.

Wani mahajjaci daga Dutse, Iliya Ahmad, ya bayyana cewa Hajji ɗaya ne daga cikin rukunan Musulunci da ya wajaba ga duk wanda yake da hali. Ya ce Alƙur’ani ya bayyana cewa addu’o’in mahajjata za su samu karɓuwa.
Ya ƙara da cewa wannan tabbaci kaɗai yana ba shi cikakken natsuwa da gamsuwa wajen fuskantar duk wani ƙalubale da ke tattare da aikin Hajji.
Mahajjatan sun kuma bayyana cewa kasancewarsu baƙin Allah na musamman saboda amsa kiranSa da zuwa Hajji, babu wata wahala ta tafiya mai nisa, zafin rana ko cunkoso da zai hana su gudanar da wannan ibada.

Malamai sun bayyana cewa, duk wanda ya gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata, za a gafarta masa zunubansa kuma ya zama tamkar sabon jariri mara laifi.
A wata hira da Rediyon Najeriya, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce an samar da dukkan abubuwan da suka dace domin jin daɗin mahajjatan jihar a Arafat.
A cewarsa, za a kai mahajjatan zuwa Dutsen Arafat cikin dare.
Ya ce, “An samar da tantuna masu na’urar sanyaya iska tare da katifu, matasan kai da barguna ga kowane mahajjaci. Haka kuma saboda zafin rana, an sanya na’urorin sanyaya ruwa a tsakanin tantuna domin rage haɗarin rashin ruwa a jikin mahajjata.”

Labbo ya ƙara da cewa za a kuma samar da abinci sau uku a rana tare da ruwan sha, da lemu da ‘ya’yan itatuwa ga mahajjatan jihar.
Ya shawarci mahajjatan da su fara da tsoron Allah a zukatansu, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko wajen gudanar da Hajji cikin sauƙi da nasara.
Ya ce, “Annabi (SAW) ya gudanar da Hajji ta hanyar tafiya zuwa Mina bayan fitowar rana a ranar 8 ga Zul-Hijja, amma saboda yawan mahajjata, yanzu ana fara jigilar su tun daga tsakiyar daren ranar 7 domin tabbatar da isa a lokacin da ya dace.Haka kuma ana kai su Arafat ranar 8 ga wata da daddare domin kauce wa jinkiri.”
Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, jami’an Mu’assasa na Saudiyya na ci gaba da gudanar da cikakken bincike ga kowane mahajjaci kafin ba shi damar shiga motocin da Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa ta tanada domin kai su Dutsen Arafat.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
