Labarai
Kwastam Ta Yi Taro da ‘Yan Jarida kan Tsaro da Wayar da Kai
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bukaci ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin ta da kafafen yaɗa labarai domin inganta wayar da kan jama’a, tsaron iyakoki da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
An bayyana wannan kiran ne a yayin Taron Tattaunawa na Zone B da aka gudanar a Kano mai taken: “Gina Haɗin Kai Tsakanin Kafofin Yaɗa Labarai da Kwastam domin Ƙara Fahimtar Jama’a da Ci gaban Ƙasa.”
Da yake jawabi a taron, mukaddashin Kwamandan Kwastam na Kano/Katsina, Usman Adamu, ya ce taron wata dama ce ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin Hukumar da ‘yan jarida.
Ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen sanar da jama’a ayyuka da manufofin Kwastam, tare da jin daɗin goyon bayan da suke ba Hukumar.
A jawabin maraba, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kwastam Kano/Jigawa, CSP Tahir Balarabe, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa sadarwa da inganta yaɗa bayanai ga jama’a.
Ya ƙara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen ƙara fahimtar da jama’a game da ayyukan Hukumar da nauyin da take aiwatarwa.
Haka kuma, Mai Magana da Yawun Hukumar na Kasa, DCC Abdullahi Maiwada, ya yaba wa ‘yan jarida bisa goyon baya da haɗin kai da suke ba Hukumar.
Ya jaddada muhimmancin yaɗa sahihin labarai, yana mai cewa Hukumar na ƙara amfani da fasahar zamani domin inganta ayyukanta da tabbatar da ingantaccen bayani ga jama’a.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
