Labarai
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
Daga Nasir Malali
Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane huɗu da ake zargin mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa a Jihar Sakkwato.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar, Laftanar Janar Aliyu Danja, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce dakarun sun samu nasarori a wasu ayyuka daban-daban da suka gudanar a sassan jihar, da nufin dakile ayyukan ‘yan ta’adda.
A ranar 20 ga watan Satumban 2026, dakarun sun kai dauki a harin da ‘yan ta’adda suka kai Sabon Gari a Ƙaramar Hukumar Wurno, inda suka yi musayar wuta da maharan tare da tilasta musu ja da baya. Dakarun sun kuma ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kai wani farar hula da ya samu raunin harbin bindiga asibiti.
A wani samame, dakarun sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kusa da Chabe Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, bayan samun bayanan sirri kan yunƙurin da suke yi na ratsa hanyar Sabon Birni zuwa Takatsaba. Haka kuma, an ceto wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su bayan artabu da ‘yan ta’adda a hanyar Isa zuwa Kwanar Isa zuwa Shinkafi. Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ya samu karaya an kuma kai shi Babban Asibitin Isa.
A Ƙaramar Hukumar Illela kuwa, dakarun sun kama mutane huɗu da ake zargin mambobin Lakurawa ne, bayan samun bayanan sirri kan yadda suke tafiya da garken shanun da aka sace daga ƙauyen Sarma zuwa Illela. An kuma kwato shanu shida a yayin samamen.
Sanarwar ta ce nasarorin sun nuna tasirin ayyukan dakarun da ke amfani da bayanan sirri wajen dakile ayyukan ta’addanci, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma hana ‘yan ta’adda damar zirga-zirga cikin sauƙi a yankin da ake gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
