Kasuwanci
Gwamnatin Sakkwato Ta Kashe Naira Miliyan 60 Kan Koyon Sana’o’i
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da rabon kuɗaɗe har Naira miliyan sittin ga matasa dari shida da aka horas a sana’o’i daban-daban a ƙarƙashin shirin koyon sana’o’i na jihar.
A yayin bikin miƙa takardun cekin kudin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin, gwamnan jihar, wanda Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Cigaban Al’umma, Alhaji Garba Maitumbi Kebbe ya wakilta, ya bayyana cewa shirin horaswar an tsara shi ne domin ƙarfafa matasa su dogara da kansu tare da ba da gudummawa wajen bunƙasa ci gaban jihar.
Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa na da cikakken ƙuduri na tallafa wa bunƙasar ƙananan da matsakaitan masana’antu, a matsayin muhimmin ginshiƙi na bunƙasar tattalin arzikin jihar.
A nata jawabin, Babbar Sakatariyar Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta Jihar Sakkwato (SOSMEDA), Hajiya Binta Usman, ta ce waɗanda suka amfana da shirin—waɗanda SOSMEDA tare da Sashen Cigaban Al’umma suka horas—sun karɓi Naira dubu ɗari-ɗari kowannensu tare da kayan aikin sana’a domin tallafa musu wajen fara kasuwanci.
Ta ƙara da cewa hukumar ta riga ta horas da matasa sama da dubu uku da ɗari bakwai da hamsin a faɗin jihar.
NASIR MALALI
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
