Ilimi
NOUN Da Hukumar Gidajen Gyaran Hali Sun Buɗe Cibiyar Karatu A Kebbi
Jami’ar Karatu daga guda tare da haɗin gwiwar Hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa sun buɗe cibiyar karatu ta farko a yankin Arewa maso Yamma a gidan gyaran hali na jihar Kebbi.
Kwanturolan Hukumar Gyaran Hali ta jihar Kebbi, Yusuf Hamisu, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da cibiyar a gidan gyaran hali na maza da ke Birnin Kebbi.
Ya ce cibiyar za ta bai wa fursunoni damar samun ilimin gaba da sakandare da kuma horaswar sana’o’i domin gyara rayuwarsu kafin komawa cikin al’umma.
A cewarsa, an samar da kayayyakin koyarwa da na ilmantarwa a cibiyar, inda za a rika koyar da darussa kamar ilimin laifuka da kimiyyar na’ura mai kwakwalwa da harkokin tsaro.
Wakiliyar shugaban jami’ar NOUN, Dakta Shakirat Omoniyi, ta ce haɗin gwiwar na da nufin taimaka wa fursunoni su zama nagartattun ’yan ƙasa bayan sun kammala zaman gidan yari.
Shi ma Sarkin Gwandu, Muhammad Iliyasu Bashar ta bakin wakilinsa, ya yaba da wannan ci gaba, yayin da wasu daga cikin fursunonin suka bayyana aniyarsu ta ci gaba da karatu kafin cikar wa’adin zaman su a gidan yari.
Sani Haruna Dutsinma/Kebbi
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
