Labarai
NSCDC Ta Kama Wani Mutum da Sayar da Gurbataccen Taki a Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Hukumar Tsaro da Kiyaye Haddura ta Kasa, NSCDC, reshen jihar Zamfara, ta gabatar da wani mutum mai shekaru 33 da haihuwa bisa zargin hannu a hada da rarraba gurbataccen takin zamani a jihar.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, ASC I Umar Mohammed Mansur, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a hukumar ta NSCDC da ke Gusau, babban birnin jihar.

Mansur ya bayyana sunan wanda ake zargin da Mustafa Sani, wanda aka kama ranar 9 ga watan Mayun 2026, a unguwar Dallatu da ke Gusau.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne tare da buhuna 550 na takin da ake zargin na gurbataccen taki ne, wadanda aka sanya a cikin buhunan bogi masu dauke da sunayen kamfanoni domin rarrabawa ga manoma da dillalai ba tare da sun sani ba.
A cewarsa, laifukan da ake zargin sun hada da hada baki wajen aikata laifi, hada da sayar da gurbatattun kayayyaki, mallaka da amfani da buhunan taki na bogi, sanya bayanan karya, yaudara, da kuma niyyar damfarar jama’a.

Kakakin na NSCDC ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa yana da hannu a wannan haramtacciyar sana’a, sannan ya ambaci wasu abokan aikinsa biyu da ya kira Alhaji Yusuf da Abdulrahman Ibrahim, wadanda har yanzu ake nema ruwa a jallo.
Umar Mansur ya bayyana cewa yaduwar takin na jabu na kawo babbar barazana ga yawan amfanin gona da kuma tattalin arzikin manoma a jihar.
Ya sake jaddada kudirin rundunar karkashin jagorancin Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, na ci gaba da yaki da zagon kasa ga tattalin arziki, damfara da sauran ayyukan ta’addanci a fadin kasa.
Kakakin ya kara da cewa rundunar jihar Zamfara karkashin jagorancin Kwamanda Sani Mustafa ta dauki matakan kariya domin dakile hada da rarraba kayan noma marasa inganci.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
