Connect with us

Labarai

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Nemi a Gaggauta Hukunta Masu Safarar Yara

Published

on

Daga Nasiru Malali

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Dr Muhammad Sa’ad Abubakar NSCIA, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an gaggauta gurfanar da masu safarar yara da masu aikata cin zarafin jinsi domin rage wannan matsala.

Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a Sokoto yayin bikin cika shekaru 20 da kafuwar Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa, NAPTIP, reshen shiyyar Sokoto. Ya ce jinkirin tabbatar da adalci na kara wa masu aikata irin wadannan laifuka karfin guiwar ci gaba da munanan ayyukan.

Dr Sa’ad Abubakar, wandaSarkin Yakin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabi ya wakilta,  ya jaddada cewa ya zama wajibi iyaye su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu duk kuwa da halin da ake ciki.

A sakonsa na fatan alherin, Kwamandan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, a jihar Sokoto, Mustapha Gidado, ya roki NAPTIP da ta taimaka wajen tsaftace jihar Sokoto, ta hanyar tabbatar da aiwatar da Dokar Kare Hakkin Yara, musamman ta hanyar hukunta iyayen da ke barin ‘ya’yansu suna yawo kan tituna suna bara da sunan almajiranci.

Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa ake ganin ana jinkirta tabbatar da adalci, Babban Alkalin Jihar Sokoto, Justice Mohammed Saidu Sifawa, wanda Babban Magatakardar Kotun jihar, Aliyu Jafar Mohammed, ya wakilta, ya ce akwai dalilai da dama da ke haddasa jinkirin da wasu ke gani.

A cewarsa, gaggauta shari’a ba tare da bin ka’ida ba na iya haifar da rashin adalci, saboda doka ta tanadi bai wa duk wanda ake tuhuma damar kare kansa cikin adalci, baya ga jinkirin da ake samu daga matakan shigar da kara, bincike da sauran hanyoyin shari’a da sai an bi cikin tsanaki.

Babban Alkalin ya kara da cewa NAPTIP babbar abokiyar hulda ce wajen gudanar da harkokin shari’a.

A nata jawabin, Darakta Janar ta NAPTIP, Hajiya Binta Lami Bello, wadda Misbau Iya Kaura ya wakilta, ta tabbatar da cewa hukumar ta gudanar da bincike tare da samun nasarar hukunta masu laifukan safarar mutane da dama, lamarin da ke zama babban darasi ga sauran masu niyyar aikata irin wadannan laifuka.

Ta ce hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, masarautu, shugabannin addini da na al’umma, da kuma kungiyoyin ci gaba da na fararen hula, ya taimaka sosai wajen musayar bayanan sirri, tallafawa wadanda abin ya shafa da kuma samar da tsare-tsaren hadin gwiwa wajen yaki da safarar mutane a yankin Sokoto.

Darakta Janar din ta kuma yi kira da gwamnatin jihar Sokoto da ta kafa Kwamitin Yaki da Safarar Mutane, ganin cewa ana amfani da jihar a matsayin hanyar fitar da mutane zuwa wasu wurare.

Taron mai taken, “Shekaru 20 na Gaskiya, Kwarin Gwiwa da Adalci: Karfafa Hadin Gwiwa Domin Yaki da Safarar Mutane da Cin Zarafin Jama’a,” ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na rayuwa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara