Ilimi
Kungiyar ASUU Shiyar Sokoto Ta Bi Sahun Sauran Takwarorinta Game Da Barazanar Fara Yajin Aiki
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sanar da shirin shiga yajin aikin gargadi ga Gwamnatin Tarayya.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Sokoto, Shugaban ASUU na yankin Sokoto, Farfesa Abubakar Sabo, ya ce wannan mataki ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen magance manyan bukatun kungiyar tun da dadewa, yana mai gargadin cewa harkokin karatu a jami’o’in Najeriya za su tsaya cak, sakamakon yajin aiki a duk fadin kasa.
Farfesa Abubakar Sabo ya zargi gwamnati da yaudara da kuma sakaci ga bangaren ilimi.
Ya bayyana cewa kungiyar ta daina yarda da alkawuran gwamnati, yana mai cewa abin da ka iya dawo da amincewa shi ne daukar matakin gaggawa, kuma ingantattun, domin kaucewa durkushewar jami’o’in gwamnati.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa daya daga cikin matsalolin da ASUU ke adawa da shi, shi ne tsarin rancen ma’aikata da gwamnati ta gabatar. Kungiyar ta ce malaman jami’a ba sa bukatar rance, abin da suke bukata shi ne tsarin albashi mai inganci.
Yayin da yake yabawa da dakatar da kafa sabbin jami’o’i ba tare da tsari ba, ya ce ASUU ta gargadi gwamnati kan yadda ake yawaita kafa makarantu marasa cikakken shiri, tana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga ci gaban bangaren ilimi.
A cewar Farfesa Sabo, har yanzu malaman jami’a har yanzu na bin albashin watanni uku da rabi da ba a biya su ba.
Ya kara da cewa akwai wasu matsalolin da ba a magance ba ciki har da bashin karin girma daga 2018 zuwa 2024 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto; rashin tabbatar da dokar kafa Jami’ar Tarayya Gusau; rashin sakin kudi don fara aiki jami’o’in Birnin Kebbi da Zuru; da kuma rashin kafa majalisar gudanarwa a Jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari, Sokoto.
Daga Nasiru Malali
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
