Labarai
Ma’aikatan Lafiya A Zamfara Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Mako Guda
Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN), reshen Jihar Zamfara, ta ayyana yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai bisa zargin wariya a aiwatar da tsarin albashi na musamman na ma’aikatan lafiya (CONMESS).
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar na jihar, Kwamared Shamsudeen Sadeeq ya sanya wa hannu, ma’aikatan sun zargi Kwamishinar Lafiya, Dr. Nafisa Mohammed Maradun, da aiwatar da tsarin CONMESS kashi 100 ga likitoci kawai, tare da watsar da sauran ma’aikatan lafiya.
Kungiyar ta ce ta gudanar da tarurruka da dama da jami’an gwamnati, ciki har da Kwamishinar Lafiyar, da Shugaban Ma’aikata na Jihar da Kwamishinan ’Yan Sanda, amma duk ba su haifar da Da mai ido ba.
Saboda haka kungiyar ta fara yajin aikin daga daren Laraba, 10 ga Satumba, zuwa 17 ga Satumba, 2025.
MHWUN ta umarci mambobinta a cibiyoyin lafiya na matakin farko, asibitocin gwamnati da na musamman su shiga yajin aikin.
Ta kuma gargadi cewa, idan gwamnati ta kasa magance koke-koken su a wadannan kwanaki, za su shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta roki kungiyar ta janye yajin aikin, tana mai bayyana shi a matsayin abin da bai dace da lokaci ba, musamman duba da annobar amai da gudawa da ke addabar al’umma.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya, Suleiman Isah, ya fitar, Kwamishina Nafisa Maradun ta ce gwamnati ta sha alwashin inganta walwalar dukkan ma’aikatan lafiya.
Ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta amince da karin albashi ga likitoci a matsayin wani bangare na shirin inganta walwalar ma’aikata.
Kwamishinar ta musanta zargin nuna son kai, tana mai cewa tattaunawa na gudana da masu ruwa da tsaki domin samar da ingantaccen tsari ga dukkan ma’aikatan lafiya.
Dr. Nafisa Maradun ta bayyana rashin jin dadinta kan matakin yajin aikin, tare da kira ga kungiyar ta koma kan teburin tattaunawa, inda ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar a shirye take domin tattaunawa ta hanyar lumana don warware matsalolin da ke akwai.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
