Labarai
Gidauniyar Zayt Da KSCHMA Sun Sanya Almajirai 270 Cikin Shirin Inshoran Lafiya A Kano
Gidauniyar Zayt da ke tallafawa mata da yara, wato Zayt Foundation for Women and Children a turance, tare da haɗin gwiwar hukumar kula da kiwon lafiya a Kano (KSCHMA), sun sanya Almajirai 270 cikin shirin kiwon lafiya na jihar.
Gidauniyar ta yi rijistar almajirai 170 a karkashin shirin kula da lafiyar, yayin da gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin ƙarin 100 a Hausawan Danfulani, karamar hukumar Tarauni.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar KSCHMA, Dr. Rahila Mukhtar, ta ce haɗin gwiwar na da nufin bai wa yaran da ke cikin mawuyacin hali damar samun kulawar lafiya kyauta.
Ta bayyana cewa Gidauniyar Zayt ta kawo almajirai 170 tare da takardun haihuwa don saka su cikin shirin, sannan gwamnati ta ɗauki nauyin ƙarin 100.

Dr. Rahila ta ƙara da cewa yaran za su amfana da kulawar asibitocin gwamnati, daga matakin asibitin farko har zuwa na biyu.
Ta yabawa gidauniyar bisa wannan kokari, tare da kira ga sauran ƙungiyoyi da su yi koyi fa hakan.
A nasa jawabin, shugaban gidauniyar, Salisu Umar Gama, ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar nasara wajen inganta lafiyar Almajirai da yawanci su ke rasa damar samun kulawar lafiya.
Shi ma malamin tsangayar, Malam Ahmed Abubakar, ya jinjina wa wannan shiri, inda ya ce kafin wannan tallafi, Almajirai kan tara Naira goma goma duk mako domin sayen magunguna masu sauƙin kudi, amma akan kaisu asibiti idan cutar ta tsananta.
“Ina mai farin ciki da cewa da wannan shiri, an sauke musu wancan nauyin, kuma yanzu za su samu kulawar lafiya yadda ya kamata,” in ji shi.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
