Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Kwara Za Ta Horas Da Malamai Kan Dakile Shan Miyagun Kwayoyi A Tsakanin Ɗalibai

Published

on

Gwamnatin jihar Kwara tare da hadin gwiwar Gidauniyar MTN, da  Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaki da Miyagun Ƙwayoyi (UNODC), da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) za ta horar da shugabannin makarantu da malamai a wasu makarantun gwamnati don yaki da shan miyagun ƙwayoyi a tsakanin ɗaliban makarantu na firamare da sakandare a jihar.

Yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Ilori game da horon, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa matsalar shaye-shaye da jarabar miyagun ƙwayoyi na ƙara tsananta  zuwa matakin mmakarantun firamare.

Gwamnan wanda mai ba shi Shawara na Musamman, Alhaji Sa’adu Salahu ya wakilta, ya ce an shirya taron ne da nufin samun goyon bayan malamai a dukkan matakai a fadin jihar, musamman a matakin ƙananan makarantu na firamare da sakandare.

Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa wannan tattaunawa na da matuƙar muhimmanci a matsayin wani bangare na shirin gwamnati, na wayar da kan jama’a kan haɗarin shaye-shaye da suka dabaibaye  al’umma, musamman a tsakanin matasa.

Ya ce za a mayar da hankali ne kan malamai a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki, masu tsara ra’ayi, masu koyar da tarbiyya,  kuma masu gina ɗalibai tun daga farko.

A nasa jawabin, Mataimakin Kwamandan NDLEA na Jihar, Jamilu Usman, ya bayyana nasarorin da hukumar ta samu wajen yaki da shan miyagun ƙwayoyi a jihar.

Ita ma a yayin zaman taron na musamman, wakiliya kuma mai horaswa daga Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaki da Miyagun Ƙwayoyi (UNODC), Maria Ilugbuhi, ta ce malamai 30 da aka zaɓa a zagaye na farko, za su sami  horo kan darussa 12 waɗanda suka shafi gina ƙwarewa, ƙara ilimi, ƙwarewar hulɗa da jama’a, yanke shawara, da sauran ƙwarewar zamantakewa.

 

ALI MUHAMMAD RABIU

 

 

 

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara