Connect with us

Ilimi

Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan Daya Domin Kula Da Lafiyar Mutane Masu Rauni

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da biyan Naira Biliyan Daya domin ci gaba da bayar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mutane masu rauni dubu 287 a faɗin jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, waɗanda za su ci gajiyar shirin sun haɗa da yara, mata masu juna biyu, marasa galihu, tsofaffi da kuma masu nakasa a ƙarƙashin shirin kula da lafiya na J-Basic Healthcare ga al’ummar da ke da rauni a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma amince da ƙara yawan masu rijista daga 500 zuwa 1,000 a kowace mazaba.

A cewarsa, Asusun tallafin lafiya na jihar muhimmin sashi ne na shirin J-Health Basic Social Insurance, wanda aka ƙirƙira don kawar da cikas na kuɗi wajen samun lafiya ta hanyar ɗaukar nauyin kuɗaɗen hidimomi ga waɗanda ba za su iya biya ba.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa, majalisar zartarwar ta amince da ƙarin alawus alawus na kowane wata ga masu amfana da shirin tallafin malaman makarantu na J-Teach su 1,100, daga ₦30,000 zuwa ₦40,000 a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa, ƙarfafa aiki da inganta ilimi a fadin jihar.

Ya kuma bayyana cewa, amincewar ta biyo bayan buƙatar da ma’aikatar ilimi ta gaba da sakandare ta gabatar.

Sagir ya ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 134  domin biyan kuɗaɗen gudanarwa, harajin VAT, kuɗaden amincewa da guraben karatun dalibai, da kuɗin masauki ga ɗalibai 15 na zangon karatu na 2025/2026 a Jami’ar Near East da ke Cyprus.

Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira Miliyan 152 domin kuɗin alawus alawus na inshorar lafiya, kuɗin takardun  biza, da na izinin zama, da na abinci da kuma sufuri.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, jimillar adadin kuɗaɗen da majalisar ta amince da su domin ɗaliban 15  ya kai sama da Naira Miliyan 286.7 na zangon karatun 2025/2026.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara