Connect with us

Labarai

Uwargidan Shugaban Kasa Remi Tinubu Ta Kaddamar Da Gasar Muhalli Ta Miliyoyin Kudi

Published

on

Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar wata gasa ta muhalli a faɗin ƙasa wacce aka ƙirƙira domin ƙarfafa dasa bishiyoyi, tsaftar muhalli da kuma rayuwa mai ɗorewa a Nijeriya, a karkashin Shirin Ayyukan Jin Kai da Cigaban Al’umma (RHI).

A yayin ƙaddamar da shirin a taron da take yi bayan watanni 3 da matan gwamnoni, wanda aka yi tare da shugabannin RHI na jihohi, Sanata Tinubu ta bayyana gasar a matsayin kira ga iyalai, ƙungiyoyin matasa, al’ummomi da gwamnatocin jihohi da su haɗa hannu wajen gina Nijeriya.

Gasar wacce aka yi wa taken “A Inganta Yau Domin Gobe Ta Yi Kyau” ta kasu kashi uku, wacce kowannensu ke da lada mai tsoka:

Gasa ta farko ita ce ta Iyali, wacce aka fi maida hankali kan jihohin Arewa 11 da sahara ta fi shafa, inda ake karfafa  kowane iyali su dasa aƙalla bishiya ɗaya, kuma wanda suka yi nasara za su karɓi kyautar Naira miliyan 20.

Haka kuma akwai rukuni na Al’umma wanda aka buɗe wa makarantu, ƙungiyoyin matasa, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kananan hukumomi a faɗin ƙasa domin farfaɗo da wuraren da aka lalata, ta hanyar mai da su lambuna, filayen shakatawa ko wuraren muhalli. Wadanda suka yi nasara a wannan rukuni na  kyautar Naira miliyan 50.

Rukuni da karshe kuma na jihohi ne, amma banda Jihar Enugu, inda su kuma  ake bukatar mai da  hankali kan dasa bishiyoyi a tituna da manyan hanyoyi, wanda Jihar da ta fi nuna kulawa wajen kare muhalli za ta samu Naira miliyan 100.

A wajen taron, Uwargidan Shugaban Kasar ta miƙa takardar ceki na Naira miliyan 100 ga Jihar Enugu wacce aka zaɓa a matsayin “Jihar da ta yi fice a yawan bishiyoyi” saboda jajircewarta wajen dasa bishiyoyi da kuma tsaftar muhalli.

Enugu ta cancanci wannan,” in ji Sanata Remi Tinubu. “Ba wai kawai dasa bishiyoyi take ba, har da tsaftace muhalli. Idan ka shiga Enugu, kana ganin tsafta, wanda hakan abin a yaba ne matuka.”

A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin RHI, ta bayyana cewa suna aiki tare da Ma’aikatar Muhalli ta Ƙasa domin kafa kulob kulob na muhalli  a makarantun sakandare da manyan makarantu, domin ɗora matasa kan sanin muhalli da kare shi.

An tsara gasar RHI Green Nigeria Challenge  har zuwa shekara ta 2026, inda aka riga aka kafa wa’adin tura ayyuka. Ana kuma ƙarfafa masu sha’awar shiga gasar da su samu ƙarin bayani kuma su tura ayyukansu ta manhajar shirin wato www.hrinitiative.org.

 

Daga Bello Wakili  

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara