Labarai
’Yar Najeriya Ta Lashe Gasar Alkur’ani Ta Duniya
’Yar Najeriya mai shekaru 19 mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi, ta lashe gasar karatun Alkur’ani ta Duniya ta bana.
Malama Hajara ta zama Gwarzuwar Shekara ce bayan da ta samu maki 99.5 a Gasar Hashimite ta Karatun Alkur’ani da Tajwidi ta Mata ta Duniya.
Hajara, wadda ta wakilci Najeriya, a gasar karatun Alkur’ani Izu 60 da Tajwidi, ta yi nasarar doke mahaddata Alkur’ani 40 daga kashe 38 da suka fafata a gasar.
Karo na 18 da aka gudanar da Gasar Karatun Alkur’ani ta Hashemite da gwamnatin kasar Jordan ta gudanar ta kuma karbi masaukin baki.
Malama Hajara dalibar aji biyu ce a Jami’ar Jihar Gombe da kuma Makarantar Islamiyya ta Abubakar Siddiq Islamiyya da ke jihar.
Kafin yanzu, Malama Hajara Dan’azumi ce ta zo ta hudu a rukunin haddar Izu 40 a gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 34 da aka gudanar a Jihar Legas.
A waccan gasar ta samu maki 97.1 a yayin da kanwarta Maryam ta zo ta daya a rukunin Izu 10 da Tangimi; daya ‘yar uwarta Safiya kuma, ta zo ta 8 a rukunin Izu 40.
Mahaddata 41 daga kasashe 39 ne dai suka fafata a gasar da aka gudanar a kasar Jordan, wadda Hajara ta lashe.
Gwamnan jihar Gombe ya bayyana farin cikinsa tare da alfahari da wannan nasara da matashiyar ta samu a fannin Alkur’ani a duniya.
Ya bayyana jinjinarsa ga malamanta da kuma iyayenta bisa jajircewarsu da ta kai matashiyar ga wannan mataki na daukaka.
Mahaddata 41 daga kasashe 39 ne dai suka fafata a gasar da aka gudanar a kasar Jordan, wadda Hajara ta lashe.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
