Labarai
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
Kwamishina a hukumar Aikin Hajji ta kasa mai kula da Arewa maso yamma, Sheikh Muhammad Ibn Uthman ya kai ziyarar gani da ido hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Jigawa domin duba irin shirye-shiryen da hukumar tayi na aikin Hajjin bana.
A jawabinsa, Sheikh Ibn Uthman ya bukaci ma’aikatan hukumar da su sanya tsoran Allah wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bukace su da su yi amfani da kwarewarsu wajen yiwa Alhazai hidima a nan gida da kuma kasa mai tsarki.
Sheikh Ibn Uthman ya bayyana muhimmancin da rikon amana yake da shi wajen tafiyar da alamurran aikin hajji.
A nasa Jawabin, Shugaban hukumar jin dadin alhazai na jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yi wa kwamishinan jawabi kan shirye shiryen da hukumar ta yi na samun nasarar aikin hajjin bana.
Alhaji Ahmad Umar Labbo da sauran shugabannin sassa sun zagaya da kwamishinan sassa daban daban na hukumar domin ganin ayyukan da ke gudana a halin yanzu, wadanda suka hada da gyaran shelkwatar hukumar.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
