Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024.

An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na kaddamar da kwamitin gudanar da aikin Hajji na shekarar 1445AH/2024 a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da ke kwaryar birnin jihar.

Taron ya samu halartar ma’aikatan kafafen yada labarai da za su rika ba da rahoton abubuwan da ke gudana yayin  aikin Hajji  wanda   dubban maniyyata daga Najeriya da ma sauran sassan duniya baki daya ke halarta.

Shuaibu, wanda a halin yanzu shi ne sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kware a harkar yada labarai da sadarwa.

Ya kuma taba zama tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) Correspondents Chapel reshen jihar Kano, da kuma wakilin jaridar This Day.

Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban tawagar kafafen yada labarai wani gagarumin ci gaba ne, wanda ake sa ran zai yi amfani da  kwarewarsa wajen tafiyar da harkokin yada labarai na aikin hajji.

 

Sama da maniyyata 3,000 ne daga jihar Kano ake sa ran za su halarci aikin Hajjin 2024.

 

A ranar 15 ga watan Mayu ne daidake sa ran  fara jigilar maniyyata daga kasar nan zuwa kasa mai tsarki.

Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da nasara ga dukkan maniyyata, kuma nadin Shuaibu na daya daga cikin muhimman ayyukan.

 

Khadija Aliyu

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara