Connect with us

Labarai

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Published

on

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron zabbi wanda hukumomi suka ɗora alhakin safarar su zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita, musamman ƙasar Nijar.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan ma’aikatar sufurin jamhuriyar Nijar ta haramtawa motocin ɗaukar kaya da aka yi wa rajista a Benin jigilar kayayyakinsu.

Ma’aikatar sufuri da kayan aiki na son sanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ƙasashen duniya cewa an keɓe tarin kayayyakin da za su je Nijar daga tashar Lome ko kuma a ko’ina a Jamhuriyar Togo ga motocin da aka yi wa rajista a Nijar kaɗai da Togo,” in ji sanarwar da aka fitar.

Nijar dai ta karkatar da akasarin kayayyakin da take shigarwa da su ƙasar Togo, sakamakon yadda alaƙar da ke tsakaninta da ƙasar Benin, mai adawa da gwamnatin mulkin soji da ta hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, ta tabarbare.

Nijar  na zargin ƙasar Benin da ɗaukar nauyin sansanonin ƴan ta’adda na kasar Faransa da ke shirin hargitsa yankin Sahel, kamar yadda ta musanta.

Jamhuriyar Benin ta dakatar da fitar da man fetur a yayin da Nijar ke ci gaba da rufe iyakokinta duk da cewa an ɗage takunkumin da shugabannin kasashen yammacin Afirka suka ƙaƙaba mata kan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023.

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara