Labarai
Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya
Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar doya da kudinta ya kai Naira dubu dari da arba’in da hudu.
Mutumin wanda ya nemi kotu ta mishi sassauci, an yanke masa hukuncin ne kan aikata laifuka da sata.
Alkalin kotun Jacinta Okeke, ta yanke wa Sani hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu ko kuma yin aiki a kasuwar Gwagwalada.
Ta kuma gargade shi da ya guji aikata laifuka.
Tun da farko, lauya mai shigar da kara, Abdullahi Tanko, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Liasu Saidu, na kauyen Ukara, ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda a ranar 9 ga watan Mayu.
Tanko ya ce wanda aka yankewa laifin ya kutsa kai cikin gonar wanda ya kai karar ya tuge masa doyar da ya shuka wadda kudinta ya kai Naira 144,000.
A cewarsa laifin ya sabawa sashe na 348 da na 287 na kundin laifuka.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
