Labarai
Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki
Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya aikata, na bayar da bayanan da suka tabbatar da tuhume-tuhumen da suka gabatar wa kotu.
Shaidar da Cohen, ya bayar dai ta kara tabbatar da zargin masu gabatar da kara na alakar Trump da Stormy Daniels.
A baya dai an zargi Trump din da yin lalata da Stormy Daniel, kuma ya biya ta makudan kudaden toshiyar baki, don kar ta fallasa alakar da ke tsakaninsu.
Zargin da Trump din ya rinka musawa a lokutan baya, ko da yake ana ganin yana yin hakan ne don yakin neman zabensa na shugabancin kasar da ke tafe.
Yanzu haka dai Cohen, ya tabbatar da cewa an tura wa Stormy Daniels makudan kudade.
Sai dai a cewarsa, bai dauki ko wanne mataki ba sai da ya sami izini daga Trump kafin ya kai ga biyan Stormy makudan kudaden.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
