Connect with us

Labarai

Amurka ta Buɗe ƙofa ga Yiwuwar Samar da ƙasar Falasɗinu

Published

on

Donald Trump na Amurka. REUTERS – Kevin Lamarque

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai yi wani zama a Litinin mai zuwa don baiwa mambobinsa damar kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin shugaba Donald Trump na Amurka game da shirin zaman lafiyar Gaza, bayan gyara a daftarin da a yanzu ya buɗe ƙofa ga yiwuwar samar da ƙasar falasɗinu bisa sahalewar Amurka saɓanin a baya.

A makon jiya ne Amurka ta cimma jituwa da mambobin kwamitin 15 game da daftarin da ya biyo bayan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin na shekaru 2 tsakanin Isra’ila da Hamas.

Daftarin wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani ya amince da kafa majalisar ƙolin zaman lafiya ga yankin na Gaza wanda Trump zai jagoranta har zuwa ƙarshen shekarar 2027.

Ƙarƙashin wannan daftari akwai shirin nan na zamar da dakarun wanzar da zaman lafiya a Gazan da aka kira ISF wanda za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙasashen Masar da kuma Isra’ila baya ga horar da ƴansandan Falasɗinu don bayar da tsaro ga iyakokin Zirin na Gaza.

Saɓanin wancan daftarin da ya gabata, a cikin wannan sabon daftarin akwai yiwuwar samar da halastacciyar ƙasar Falasɗinu, bayan gyaran da Amurkan ta yiwa ƙudirin nata, kodayake akwai shakku kan yiwuwar tarin sharuɗɗa su biyo baya, lura da yadda gwamnatin Amurka ke adawa da ƴancin Falasɗinawa.

Bayanai sun ce Amurka da tarin ƙasashen Larabawa da masu rinjayen musulmi ciki har da Masar da Saudi Arabia da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa baya ga Turkiya da Pakistan da Jordan da Indonesia sun yi kira ga kwamitin da ya gaggauta zama don amincewa da wannan sabon daftari.

Cikin wata sanatawar da waɗannan ƙasashe suka fitar sun buƙaci zama na musamman kan ƙudirin a Litinin mai zuwa don amincewa da shi nan take, kodayake wasu bayanai sun ce Rasha ta gabatar da nata ƙudirin da ke cin karo da buƙatar Amurka.

Cikin ƙudirin na Rasha ta yi maraba da ƙoƙarin da ya kai ga tsagaita wuta a Gaza duk da cewa bata ambaci sunan Donald Trump a matsayin jagoran nasarar ba, sai dai bata amince da girke dakaru a Gaza ba.

Amurka ta yi gargaɗin cewa rashin amincewa da ƙudirinta kai tsaye na nufin dawo da yaƙi a Gaza da nufin kakkaɓe ilahirin mayaƙan Hamas.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara