Labarai
Kungiyar Rotary Ta Amince Da Gudunmawar Da Hukumar NAMCON Ta Kasa Take Bayarwa Ga Dan Adam.
Shugaban kungiyar Rotary Club na Kaduna Metropolitian, Rotarian Luqman Babatunde ya yi kira ga daidaikun jama’a da kungiyoyi su ci gaba da tallafa wa gwamnati a kowane mataki da ayyukan agaji da za su kawo karshen wahalhalun da al’umma ke ciki.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake karrama shugaban kungiyar manoman injinan noma ta kasa NAMCON, Alhaji Aliyu Waziri bisa irin gudunmawar da yake bayarwa ga bil’adama.
A cewar shugaban wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar Rotary Action for Peace, reshen jihar Kaduna, ya bayyana cewa, gudunmuwar da Alhaji Waziri ya bayar wajen taimakawa marasa galihu a cikin al’umma ba a bar su a baya ba.
Ya ce kungiyar da ke karkashin sa za ta ci gaba da zakulo tare da gane daidaikun mutane da mutanen da suka dace da irin wadannan abubuwan.
Rotarian Babatunde ya yi nuni da cewa kungiyar Rotary Club ta Kaduna Metropolitian ta tsara shirye-shiryen da za su yi tasiri kai tsaye ga al’ummar jihar Kaduna bisa tsarin Rotary club international.
Ya ce wasu daga cikin ayyukan da za a gudanar sun hada da raba tebura da kayan aiki da kayan rubutu ga yara marasa galihu da ke wasu makarantu a Kaduna da dai sauransu sannan ya bukaci jama’a da su tallafa musu.
Da yake tsokaci, Shugaban NAMCON na kasa, Alhaji Aliyu Waziri wanda shi ne Turakin Tudun Wada Kaduna, ya yaba da kokarin da kungiyar Rotary ke yi a ayyukan jin kai da taimakon al’umma.
Ya ce, karramawar da kungiyar ta ba shi, zai kara masa kwarin gwiwa wajen kara himma a fannonin Noma, Abinci da samar da ayyukan yi a cikin al’umma, musamman ma matasa, mata da yara.
VOC. Naomi Anzaku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
