Connect with us

Labarai

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai game da ma’adanai da sauran albarkatun ƙasa.

Da yake ƙaddamar da shafin na intanet, Ministan Harkokin Ma’adinai na Nijeriya Dele Alake ya ce sun ɗauki matakin ne domin rage wahalhalun da masu zuba jari daga ƙasashen waje suke sha wurin samun bayanai game da ma’adanai da ƙasar take da su.

“A baya mutumin da ke son zuba jari sai ya zo Nijeriya da kansa kafin ya samu bayanan da yake buƙata, amma yanzu yana iya samun waɗannan bayanai a shafin intanet sannan ya yanke hukunci kan ko zai zuba jari,” a cewar Ministan.

Nijeriya ce kan gaba a albarkatun man fetur a Afirka, kuma tana da tarin arzikin sauran albarkatun ƙasa irin su zinare, kuza, tama da ƙarafa, kwal, farar ƙasa, da sauransu.

 kuma yana ɗauke da bayanai kan dukkan ma’adanain da Nijeriya take da su da jihohin da ake samunsu da ma duk wasu bayanai kan yadda za a zuba jari a kan su.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sha alwashin bunƙasa fannin ma’adinan Nijeriya domin samun kuɗaɗen-shiga da rage dogaro da man fetur, tana mai cewa a halin da ake ciki wannan fanni ba ya samar da sama da kashi ɗaya na kuɗin-shigar ta.

A kwanakin baya ne Ma’aikatar Harkokin Ma’adinai ta Nijeriya ta gudanar da garambawul inda ta amince ta bai wa masu zuba jari kashi 75 na hannun-jarin kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar, tare da hana fitar da ma’adinan da ba a sarrafa ba, da haramta kamfanonin da ke haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara