Labarai
Majalisar Kasa Ta Bukaci A Tsaurara Tsaro Wajen Hakar Ma’adinai
Majalisar dattijai ta yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro da ka’idojin aiki kan ayyukan hakar ma’adinai a kasar.
Majalisar dattijai ta yanke wannan kuduri ne sakamakon wani kudiri da Sanata Muhammad Sani Musa Neja ta Gabas ya dauki nauyi tare da mayar da martani kan rugujewar wani wurin hakar zinari da aka yi a ranar Lahadi a Farin Doki a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Wurin, wanda kamfanin African Mineral and Logistics Ltd ke gudanarwa, ya ruguje sama da masu hakar ma’adinai 50 a lokacin da aka yi ruwan sama yayin da ya binne kusan 30 daga cikinsu.
Sanata Sani Musa wanda ya gabatar da kudirin ya ja hankalin majalisa kan munin lamarin, inda ya kara da cewa yana kira da a gudanar da bincike a kan lamarin a wani yunkuri na “gano duk wasu kura-kurai da suka shafi ka’idojin tsaro da aiwatar da doka a fannin.”
Bashir Mayere/Abdurrahman/Khalifa/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
