Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince da Karbo Rancen Naira Tiriliyan 1.15 Domin Cike Gibin Kasafin Kudi

Published

on

Daga Bashir Meyere

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje.

Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa.

Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya bar gibin  Naira tiriliyan 1.147, abin da ya haifar da bukatar wannan shirin neman rance.

Kwamitin ya bai wa Majalisar shawarar  amincewa da rancen cikin gida na Naira tiriliyan 1.15 domin cike gibin da ya samo asali daga karin kudin kasafin.

Kwamitin ya kuma bukaci Ministar Kudi  da Ofishin Kula da Lamuran Bashi su tabbatar da cewa an aiwatar da rancen cikin tsari, tare da bin ka’idojin gaskiya,  da sharuɗɗan da suka dace.

Majalisar Dattawa ta kuma umurci kwamitinta mai kula da bashin cikin gida da na waje da ya rika sa ido kan yadda za a aiwatar da amfani da kudin da aka ciwo bashi.

Haka kuma, Ministar Kudi za ta rika mika rahoton kowane watanni uku kan halin da ake ciki, da amfani da kudaden, da yadda ake biyan basussuka, yayin da za a kai duk wani rahoton sabawa tsarin  ga Majalisar Dattawa domin daukar matakin doka da ya dace.

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara